Wednesday, 16 November 2016

DAKARUN MUSULUNCI

🏇 DAKARUN MUSULUNCI 🏇
Na Abdul-Aziz Sani M/GINI
Written by
2 EFFECT
SUNNAH
&
TEEMERH NEW

1⋐⋑5

A wani zamani can baya mai tsawo da ya shuɗe, anyi wani shahararren sarkin Musulunci wanda ya shekara ɗari da sittin akan karagar mulki, ana kiransa da suna Uwaisul Karni. Har tsufa ya riski Sarki Uwaisul karni matan sa biyu kacal, kuma 'ya'yansa biyu dukkan su maza sa'annin juna. Ana kiran waɗannan 'ya'ya nasa da UKASHAT da UZAIFAT .
 Mahaifiyar Ukashat ita ce Uwar gida. Ukashat da Uzaifat sun taso da tarin ilimi, hankali da sanin ya kamata, sannan kuma kowannensu ya kasance Sadauki kuma barde dodon maza a filin yaki, wanda har ta kai an kasa banbancewa wanda ya fi wani karfi da jarumtaka a tsakanin su.
 Yayin da tsufa ya riski sarki Uwaisul Karni sai matansa Shulaifa da Muzaira suka fara kishi akan kowacce ta fi so ɗanta ya gaji Sarki. A dalilin haka ne suka dukufa wajen Ziyartar Malamai domin bukatarsu ta biya.



🔯🔯🔯
A can nesa da birnin DARUL HUSUF, wato birnin Sarki Uwaisul Karni, akwai wata babbar kasa ta kafirai wacce ta gagari Sarki Uwaisul Karni, domin sau tara yana yaki da su amma sai dai ayi KARE JINI, BIRI JINI. Sunan kasar SHUMBUL, kuma sunan sarkin su Sharan Ibini Nukaib.
 Lokacin da sarki Uwaisul karni ya fahimci cewa Ukashat da Uzaifat sun tada hankalinsu akan su gaje shi saboda kowanne ya ɗauki zugar mahaifiyarsa sai ya kira su ya ce da su:
"Ya ku 'ya'yana kuyi sani cewa bani da wani buri a duniya wanda yafi naga na ci birnin shumbul da yaki kafin cikar ajalina, bisa wannan dalili ne na umarceku da kuje kowannen ku ya shirya DAKARUN MUSULUNCI nasa mataimakansa waɗanda basa yin aikin Alfasha, basa shan giya, basa yin zina, waɗanda basu taɓa saɓon Ubangijin Musulunci ba, kowannenku ya taro nasa mataimakan duk wanda ya sami nasarar yaki akan kasar shumbul daga cikin ku shine zai gaje ni".
 Koda jin wannan batu sai Uzaifaf da Ukashat suka yi murna, suka yi farin ciki da jin wannan batu. Domin lokaci yayi da zasu nunawa duniya cewa Musulunci ba kanwar lasa ba ne. Anan suka yi alkawarin lalle sai sun cikawa mahaifinsu burinsa. Nan take kowannensu ya fara shirye-shirye, suna masu shirya dakarun yaki kuma DAKARUN MUSULUNCI.
 Dama sarki Uwaisul Karni ya basu izinin kowannensu ys tara dakaru dubu ɗari uku kaɗai.
 Ukashat ne ya fara haɗa tasa rundunar inda yai sauri ya ɗebe dukkanin manyan Dakarun kasar waɗanda ake takama dasu a fagen fama, wato waɗanda suka fi jarumtaka, juriya da jajircewa. Lokacin da Ukshat ke zaɓo waɗannan zaratan Dakaru baiyi la'akari da bayanin mahaifinsu ba na cewa lalle su zaɓo daga masu kwatanta gaskiya da tsoron Allah. In dai ya fahimci cewa mutum barde ne kawai sai ya zaɓe shi.
 A lokacin da Uzaifat yazo zai zaɓi nasa dakarun sai yaga ashe Ukashat yai masa shigar sauri, ya kwashe manyan baraden kasar waɗanda sune dirkar birnin masu ciyo yaki. Hatta sarkin yakin Kasar kuwa Salahuddeen Ayubi. Al'amarin da ya dugunzuma hankalinsa kenan, har ya ji gwiwarsa tayi sanyi, amma duk da haka bai fasa zaɓo nasa dakarun ba waɗanda basu kasance zakwakurai ba, amma kuma suna da karfin imani gami da tsoron Allah. Ya fitar da shugaba a cikinsu wanda babu kamar sa a jarumta, ana kiran sa da suna Abul Shaja'a.
 Bayan Uzaifat ya gama haɗa wannan runduna wadda Abul Shaja'a ke jagoranta sai suka fara fita bayan gari kullum suna bawa kansu horon yaki domin su tabbatar da cewa anyi kyakkyawan shiri kafin zuwa ranar da zasu fara fita su tari abokan gaba. A can ɓangaren Dakarun Ukashat kuwa, ko sau ɗaya basu taɓa tunanin su fita yin horo ba saboda sun yarda da kansu, sun san cewa ko daga bacci suka tashi zasu iya tarar yaki.
 A ranar da su Uzaifat suka cika kwana bakwai suna baiwa kansu horon yakin ne labari ya riski su Ukashat. Al'amarin da ya basu dariya kenan.
 Ukashat ya dubi Sarkin yaki Salahuddeen ya ce "Ya kai dirkar Darul Hasuf kaji cewa su Uzaifat sun dukufa wajen baiwa kansu horon yaki har tsawon kwana bakwai kenan yau. An ya kuwa ba ma kai musu ziyarar ba zato ba, domin mu auna iyakar kokarinsu da namu. Ka san ance ɗan hakin da ka raina shi kan tsone maka ido. Kada fa muyi sakaki su bamu mamaki, wato su sami nasarar wannan yaki da za a yi da mutanen Shumbul".
 Koda jin wannan batu sai Sarkin Yaki Salahuddeen Ayubi ya bushe da dariya ya ce, "Ranka ya daɗe in banda abinka yaya gara za tayi da zago? Shin ka manta da yawan mayakan birnin Shumbal ne da kuma yawan yawan zakwakuran dakarunsu ne, ai duk irin horon da su Abu Shaja'a zasu samu ba za su taɓa samun nasara ba a kansu. Mu ma kanmu nan sai munyi da gaske, mun yi tunanin sabbin dakarun da ya kamata muyi amfani dasu. Ka sani cewa a cikin mayakan birnin Shumbal akwai wani gawurtaccen barde da ya fara fitowa yaki a shekaru uku baya. Wannan barde shi nafi shakka fiye da kowa, kuma babu yadda za ayi mu sami nasara akan mutanen Shumbal face mun gama da barden."
 Yayin da Ukashat yaji wannan batu sai ya jinjina kai ya ce, "Menene sunan barden, kuma ya za ayi na shaida shi idan muka fita yakin? Ima son ka barni da shi, ina tabbatar maka da cewa ni zan kashe shi komai karfin Jarumtakarsa."
 Da jin wannan batu sai Salahuddeen Ayubi yai dariya ya ce "Ya kai yarima Ukashat ka sani cewa sau uku ina tarar wannan barde fa muna yin ragas, ban taɓa samun nasara akansa ba, shima haka. Ta ya ya kake tsammanin cewa kai zaka iya dashi?"
 Ukashat yayi murmushi ya ce, "Ina da tabbacin zan iya samun nasara a kanka, ka ga kenan idan har zan samu a kanka lalle zan samu a kansa. Na fuskanci cewa saboda bamu taɓa fita yaki ba ni da Uzaifat shi ya sa ba a san iyakar jarumtakarmu ba, sai iya wadda aka ga mun nuna anan gida. Idan kana shakkar abinda na faɗa yanzu mu jarraba fidda raini yanzu ni da kai"



6 ♦10


Sa'adda Sarkin yaki Salahuddeen Ayubi yaji haka, sai ransa ya ɓaci, zuciyarsa ta kama tafarfasa ya ce a ransa _"Yanzu wannan karamin yaron Ukashat da ya girma a gaba na shine yake ganin cewa zai iya karo da ni? Lalle kuwa yau zan nuna masa cewa bakin rijiya ba wajen wasan yaro bane."_ 
 Koda gama aiyana hakan a ransa sai ya zare takobinsa ya sauko daga kan dokinsa a fusace ya nufi Ukashat. Abinda ya ɗaurewa sauran Dakarun kai shine, Ukashat ba zare tasa takobin ba bare ma ya sauko daga kan nasa nasa dokin, kawai sai ya ci gaba da zamansa yana mai sauraron isowar Salahuddeen. Ai kuwa Salahuddeen na isowa sai ya kai masa wawan sara a wuya. Cikin matukar zafin nama Ukashat ya sunkuya takobin ya sari Iska.
 Kafin Salahuddeen ya sake kai wani saran tuni Ukashat yai tsalle sama daga kan dokinsa tamkar an janyeshi da kugiya kawai sai ya jerawa Salahuddeen duka da Kafa a kirji sau uku yana a saman kamar tsuntsu. Duk da cewa Salahuddeen murjejen kari ne mai kirar sadaukantaka sai da yayi baya taga-taga zai faɗi, amma saboda taurin rai da zuciya sai ya dage ya tsaya cak a waje guda. A sannan ne fa gaba ɗayan dakarun suka kaure da kabbara bisa mamakin ganon jarumtakar da Ukashat yayi.
 Shi kansa Salahuddeen yai mamaki, duk da cewa ya sha ganin yadda Ukashat da Uzaifat ke dakawa maza gumba a hannu a cikin gari, amma da yake suna shakkarsa sai yayi tsammanin cewa ba zaau iya karawa da shi ba. Abin da bai sani ba shine kawai suna girmamashi ne a matsayinsa na Sarkin Yaki kuma basa so su kunyatashi.
 Ukashat ya diro kasa a bayan Salahuddeen ya zare tasa takobin suka fara zagaya juna suna kallon kallo tamkar Zaki da Zaki zasu kafsa. Kawai sai suka kacame da azababben yaki suna masu kaiwa juna *SARA DA SUKA* cikin zafin nama, juriya da bajinta tamkar masu jikin karfe saboda sauri. Nan fa dakaru suka zuba ido suna kallon ikon Allah suna al'ajabi, domin a tarihin sadaukantakar Salahuddeen ba a taɓa samun mutumin da ya fafata da shi ba tsawon dakika ɗari da tamanin ba tare da ya kaishi kasa ba, sai wannan bakon barde na birnin Shambul, amma yanzu gashi Ukashat na neɓan gagararsa.
 Abu dai kamar wasa sai gashi an sake shafe rabin sa'a ana wannan fafatawa amma duk a tsawon lokacin ko sau ɗaya Salahuddeen bai sami damar yankar jikin Ukashat ba ko sukarsa. Al'amarin da ya kara fusatashi kenan ya kara kaimi. Yayin da Ukashat ya ga haka sai yayi wata irin alkafira da baya-baya ya nisanta da Salahuddeen ya tsaya daga nesa kaɗan fuskarsa cike da murmushi yace, "Ya kai Sarkin yaki kayi sani cewa na baka dama har tsawon sama da rabin sa'a ba ka iya cutar dani ba, to yanzu gani nan bisa kanka nima zanyi amfani da tawa damar."
 Kafin Sarkin yaki Salahuddeen yayi wani yunkuri tuni Ukashat ya daka tsalle ya dira a gabansa kamar ɗaukoshi akayi aka ajiye. Nan fa ya shiga kaiwa Salahuddeen mummunan sara da suka. Tsanannin karfin harin yasa Salahuddeen kasa mai da martani, sai kawai ya ci gaba da kare kai. A duk sa'adda Ukashat ya sami damar cutar da Salahuddeen sai ya ki cutar dashi dan yayi dariya kawai. A haka suka ci gaba da artabu har Ukashat ya kaishi kas kuma ya buge takobinsa ta faɗi kas ya tsirashi da tasa. Kawai sai sauran Dakarun suka ruɗe da kabbara suna yiwa Ukashat jinjina cikin matukar al'ajabi.
 Ukashat ya juyawa Salahuddeen baya ya tafi izuwa dokinsa ya kama ya hau, sannan ya juyo ya dubeshi ya ce, "ku biyoni a baya mu tafi izuwa bayan gari inda su Uzaifat ke baiwa kansu horo."
 Gama faɗin haka ke da wuya sai Ukashat ya sakarwa dokinsa linzami ya sukwaneshi da gudu ya bar harabar gidan sarautar. Cikin alamun kunya da matukar takaici sarkin yaki Salahuddeen ya mike tsaye ya hau kan nasa dokin a lokacin da kwallar takaici ta cika idanunsa, amma kuma da ya ga sauran Dakarun sun tsaitsaya a bayansa sai da ya hau dokinsa yai gaba sannan suka take masa baya sai yaji daɗi a ransa, domin ya fahimci cewa har yanzu yana da sauran kima da martaba a idanunsu duk da cewa yarima Ukashat ya kaskantar da shi a gabansu
 Sarkin yaki Salahuddeen da sauran Dakarun suka zaburi dawakansu a guje har suka cimma Ukashat, ya zamana cewa Ukashat da Salahuddeen sun kusan haɗa kafaɗa. A sannan ne Ukashat ya dubi Salahuddeen ya ce "Ka gafarceni ya dirkar Darul Husuf, kayi sani cewa bani da niyyar kaskantarka akan idon kowa."
 Koda jin wannan batu sai Salahuddeen yaji zuciyarsa tayi sanyi ya maida masa martanin murmushi sannan yace, "Ya shugabana ai kome kayi mini ba zai taɓa zama laifi ba, domin kaine sarkin gobe. Fatana shine idan har bukata ta biya na zamo mukasanci a gareka."
 Sa'adda Ukashat yaji haka sai ya bushe da dariya, daga can kuma sai ya haɗe fuska yace, "idan har ka taimaka mun wannan runduna tamu ta ci birnin shumbul da yaki nayi maka alkawari kaine zaka zama wazirina yayin da na zama Sarkin Darul Husuf."
 Koda jin haka sai Salahuddeen ya cika da tsananib farin ciki, ya kara bakinsa daf dana yarima Ukashat yace, "Ai kuwa ko da zan kauce hanya sai na kauce muddin bukatarmu zata biya, saboda haka ka kwantar da hankalinka komai rintsi da tsanani kai ne zaka hau karagar Sarki, ba dai Uzaifat ba sai dai idan bana numfashi a doron kasa."Sarkin yaki Salahuddeen da sauran Dakarun suka zaburi dawakansu a guje har suka cimma Ukashat, ya zamana cewa Ukashat da Salahuddeen sun kusan haɗa kafaɗa. A sannan ne Ukashat ya dubi Salahuddeen ya ce "Ka gafarceni ya dirkar Darul Husuf, kayi sani cewa bani da niyyar kaskantarka akan idon kowa."
 Koda jin wannan batu sai Salahuddeen yaji zuciyarsa tayi sanyi ya maida masa martanin murmushi sannan yace, "Ya shugabana ai kome kayi mini ba zai taɓa zama laifi ba, domin kaine sarkin gobe. Fatana shine idan har bukata ta biya na zamo mukasanci a gareka."
 Sa'adda Ukashat yaji haka sai ya bushe da dariya, daga can kuma sai ya haɗe fuska yace, "idan har ka taimaka mun wannan runduna tamu ta ci birnin shumbul da yaki nayi maka alkawari kaine zaka zama wazirina yayin da na zama Sarkin Darul Husuf."

 Koda jin haka sai Salahuddeen ya cika da tsananib farin ciki, ya kara bakinsa daf dana yarima Ukashat yace, "Ai kuwa ko da zan kauce hanya sai na kauce muddin bukatarmu zata biya, saboda haka ka kwantar da hankalinka komai rintsi da tsanani kai ne zaka hau karagar Sarki, ba dai Uzaifat ba sai dai idan bana numfashi a doron kasa."


11⋐⋑15

Da jin haka sai shima Ukashat ya cika da murna suka ci gaba da hira cikin nishadi har suka iso bayan gari inda su Uzaifat suka yada sanasani suka kafe tantuna. Da zuwa kuwa sai suka iske Uzaifat tare da dakarunsa yana tsaye a tsakiyarsu sun yi masa da’ira yana koya musu yadda ake sarrafa takobi a tsakiyar abokan gaba, harma yana umartar wasu daga cikinsu da su afka masa. Da zarar sun afka masa sai su ga ya tarwatsasu nan da nan. Suna cikin wannan hali ne kawai sai suka hango kurar dawakan su Ukashat daga nesa kadan don haka sai suka tsaya suna jiran isowarsu don su ga ko su waye. In ba don ma sun ga cewa daga cikin gari suka fito da sai suyi tsammanin ko abokan gaba ne suka kawo farmakin sumame.
Lokacin da su Ukashat suka karaso aka ga juna sai mamaki ya kama Uzaifat ya dubi Ukashat y ace, “Lale marhabun da dan Uwa rabin jiki. Shin kun zo ne ku bamu gudunmawa bias kokarin da muke yi?”.
Ukashat ya kada kai alamar cewa ba wannan ce ta kawo su ba, sannan yace, “Mun zo ne mu yi liken asirinku mu saci irin salon yakin da kuka tanada”.
Ko da gama fadin haka sai mamaki ya kama Uzaifat da jama’arsa, domin sun san cewa basu fi su Ukashat iya yaki ba, asali ma ko tafin hannunsu ba su kai ba.
Ukashat da jama’arsa suka bushed a dariya, al’amarin da ya sosa zuciyar Uzaifat kenan. Amma sai ya dubi Ukashat yace, “Ya kai dan uwana ina son ku bar wajen nan kai da jama’arka ku kyalemu mu yi abinda ke gabanmu mu da ku kowa tasa ta fishsheshi.”
Ukashat ya gyada kai yana mai yin murmushin mugunta yace, “Ba zai yiwu ba muzo har nan kuma mu tafi a banza. Mun zo ne domin jama’ata da taka su gwada ‘yar kasha domin a bambance tsakanin aya da tsakuwa, asan wadanda ya kamata a tura yaki ba sai an tsaya bata lokaci ba”.
Cikin fushi Uzaifat ya dakawa Ukashat tsawa yace, “Wannan ai zancen banza ka ke yi, domin kuwa bah aka Abbanmu ya shirya ba. Cewa yayi ni da kai kowannenmu ya shirya dakarunsa dabam, kuma dukkaninmu zamu je wannan yaki, bai zaba ba”.
Ukashat yai dariya sannan yace “Wannan gaskiya ne, haka Abbanmu ya tsara amma kuma nima yanzu nazo da nawa tsarin kuma dole haka za a yi”. 
Koda gama fadin haka sai Ukashat ya dubi su Sarkin yaki Salahuddeen yace “Ku afka musu ku maishe da su nakasassu yadda ba za su iya fita yaki ba.”
Koda jin wannan Umarni sai su Salahuddeen suka zare makamansu da nufin su afkawa su Uzaifat, amma sai Uzaifat yayi wuf ya sha gabansu yace “Ku fara gamawa da ni kafin su”.
Da jin haka sai su Salahuddeen suka dan ja baya domin sun san cewa abu ne mai hadarin gaske idan dayansu ya kuskura ya taba lafiyar yarima Uzaifat.
Ukashat ya dakawa su Salahuddeen tsawa yace, “Me kuke jira ne dashi? Ku afka masa kawai, umarnina ne ban a kowa ba”. Cikin sanyin jiki da alamar karayar zuciya Sarkin yaki Salahuddeen ya dubi Ukashat yace, “Ya shugabana kai ma ka san cewa duk wanda ya taba yarima daga cikinmu zai fuskanci fushin sarki. Ina ganin cewa zai fi kyau mu hakura da wannan shiri mu koma cikin gari”.
Koda jin wannan furuci sai Ukashat ya fusata, ya zare takobinsa ya nufi Uzaifat gadan-gadan yana mai cewa, “Ni bari na nuna muku misali ku ga zahiri, don ku san cewa baba wargi a cikin lamarina”.
Lokacin da Uzaifat ya ga dan uwansa Ukashat ya taho kansa rike da takobi tsirara cikin mugun nufi sai shima ya zare tasa takobin ya tare shi a lokacin da gaba daya dakarun da ke wajen suka nutsu suka tattara hankulansu kowa a kansu.

 'Yan uwan biyu na haduwa suka kaure da azababben artabu, ya zamana cewa suna kaiwa juna sara da suka cikin zafin nama, juriya da bajinta.
Wohoho! Idan sadaukantaka ta hadu da takwararta dole ne idanu su more kallo. Lokacin da wannan gumurzu ya dan yi nisa sai hankalin gaba daya Dakarun da ke wajen ya dugunzuma ainun, domin tsanani ya kai tsanani, ga dukkan alamu ba za a gama lafiya ba ba tare da an salwantar da rayuwar daya ba. Domin yadda suke kaiwa juna hari tamkar kafiri da musulmi sun hadu, kowannensu bil hakki yake fadan kuma a fusace suna kokarin ganin bayan juna.
Koda aka shafe rabin sa'a ana wannan fafatawa sai suka ja da baya a lokaci guda suka ba da tazarar taku biyar-biyar, sannan suka rugo ga juna cikin mugun nufi. Tun kafin su hadu hankalin kowa dake wajen ya kara dugunzuma, domin an san cewa in dai aka hadu karon ba zai yi kyau ba. Ko da ya rage saura taku daya su hadu sai suka daka tsallesuka yi sama a lokaci guda suka kaiwa juna sara da takobi. Kowa sai ya sami nasara suka yanki damatsan hannayensu, jikinsu ya dare jini ya zuba suka rikito kasa suna masu dafe raunukan.
Amma saboda juriya da jarumtaka basu nuna wata gazawa ba, sai kawai suka sake yunkurawa suka ruga ga juna.
Cikin zafin nama Sarkin yaki Salahuddeen ya daka tsalle ya dira a tsakiyarsu, bai bari sun hadu ba. Cikin fushi Ukashat ya dakawa Salahuddeen tsawa yace, "Saboda me zaka katse mana wannan fada?".
Salahuddeen ya risina sannan yace, "Ka gafarceni ya shugabana, kayi sani cewa idan muka bari kuka lahanta junanku sosai fushin mahaifinku zai tabbata akanmu. Idan kaga mun barku kun ci gaba da wannan gasa sai dai idan bama numfashi a doron kasa."
Sa'adda Ukashat yaji wannan batu sai takaici ya kamashi ya rasa abinda ke masa dadi a duniya, kawai sai ya yi tsaki ya juya ya tafi ga dokinsa ya kamashi ya hau ya sukwaneshi a guje.

Saturday, 5 November 2016

HALACCI

[22/10 6:21 PM] Eshart Tsafe : *KINMAN HALACCI* © By *ESHART TSAFE* Page 1⃣➖2⃣*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI,TSIRA DA AMINCI SUTABBATA GA SHUGABANMU KUMA ANNABINMU ANNABI MUHAMMAD SHIDA ALAYANSA DA SAHABBANSA BAKI DAYA AMEEN.* Wanna shine hukuncin da nayanke in kuma so kake kanuna man ban isa da ariana bane fine bazan tilas takaba tunda kaine mahaifinta, haba yaya Allah yasa wake hakan tafaru wlh banufina kenanba kawai ina duba yuwowar abun ne sai inga kamar za'a shiga hakkin Abdallah ne amma inbanda haka ba abunda zaisa in musa maka, amma dan Allah kayi hakuri banyi haka daniyar bata makaba.
Ko kaifa banason kana cewa haka, idan kau har hakane to ta tabbata bamu muka haifesa bakenan ai yazamar masa dole yaso abunda mukeso yakuma bi umur ninmu matukar yanason gamawa da duniya lfy. Hakane yaya todan haka addu'ar ka kawai muke nema tare da fatan alheri,
Allah yasanya alkeri ya hada kansu yasa muce kara da akayi, Allah kuma yabar zumunci ameen ameen kanina,
To inaga tunda gobene za ai addu'ar bakwai sai ahada da daurin auren baki daya tunda ba abunda zamu tsaya jira Hakane Allah yakaimana rai goben, ameen.
Masha Allahu amma gaskiya alhj kayi tunani mai kyau kuma hakan shine daidai, dama tunanina gobe idan zamu wuce to bazan bartaba dole muwuce tare da ita to ashema tare da sarakuwata zanwuce gaskiya nayi matukar farin ciki dasa mun sarakuwa irin ariana kuma bakaramin dacen mata yaronnan yayiba , yarinya mai hankali da natsuwa bazaka taba cewa tashin kauye bace sosai mahaifiyarta tayi kokarin bata tarbiya maikyau, Allah sarki karima ashe bazakiyi tsawon raiba Allah ya gafarta maki yayi maki rahama yakuma kyautata makwancinki yasa halinki yabiki ameen.
Ariana zaune gaban abbanta kanta a kasa tana kokarin maida hawayenta, hannu yasa yadago kanta ariana kuka kike?
Kai ta girgiza alamar a'a auren ne bakiso? nanma kai ta girgiza to gayaman miyasa kike kuka shiru tayi batare da tace komiba yadade yana nazarinta kan yace ko yayan nakine baki so?
Da sauri tadaga mai kai alamar eh shiru yayi nadan wani lkc tabbas yasan ita da Abdallah basa shiri ko kadan hasalima basa shan inuwa daya kasan cewarshi mai tsananin son girma bazaka taba ganin dariyarshi ba muddun kannanshi nawurin amma bayan haka baisanshi da wani hali marar kyauba kuma da ace mahaifiyarta naraye ne datafi kowa farin ciki saboda akwai tsananin shakuwa da fahimtar juna tsakanibta da shi.
Baisan yadda zai karbi zancenba
Saidai fatanshi Allah ya daidaita tsakaninsu yasanya masu kaunar junansu.
To yishiru share hawayenki da sauri tasa hannunta tashiga share fuskarta, kinajina ko kai tadaga mashi
Banason kina cewa bakya son dan uwanki domin shi jininkine kuma garkuwa agareki sannan abun alfaharinki banason kina tada hankalinki akan abunda baikai yakawo ba insha Allahu bazaki taba dana saniba nasan dan uwanki bazai taba cutadda keba nasani zairikeki da amana bazai taba barin wani abu yasamekiba..
Amma abba aibaya sona hasalima ya tsaneni da bakinshifa yataba fadaman hakan to abba taya kake tunanin zai soni kuma har yayi zaman aure dani?
Abba dan Allah kada kabari a hadani dashi wlh mugune bayada tausayi baikamaci zama abokin rayuwataba abba dan Allah ka tausayaman,
Hannuwanta yakamo dake rike da kafafunshi ba abunda zanyi da yawuce inbaki hakuri inkuma yimaki addu'ar fatan alheri a duk inda kika kasance, kinfi kowa sanin banida kowa a duniyar nan da yawuce yaya shikadai yarageman dan haka dole in mashi biyayya inada tabbas din yaya bazai taba zama maki abunda zai cutar dake ba dan haka nike umurtarki dakizama mai biyayya, kizama mace tagari a cikin dakin aurenki mai hakuri gaduk wani abu da zaki gani matukar kikai hakuri to zaki cimma iyakar koma minene abu nagaba danike horonki dashi kizama mai rike sirrinki dana mijinki banason kizama cikin shasha shan matan dake fallasa sirrin gidan mazajensu duk runtsi kiyi kokarin rike sirrinki,
Maganar zaman takewa kuma basai nace maki komiba nasa mahaifiyarki tana koya maki wani abun kuma kema kina ganin yadda take tafiyar da rayuwar aurenta to inason kiyi koyi da ita dan ita macece tagari wadda kowane namiji zaiyi alfahari da samunta,
Cikin kankanin lkc yanayinsa ya chanja kwalla tacikamai ido cikin dubara ya gogeta batare daya bari yar tashi ta fahimci hakanba, tabbas ina kyautatama mahaifiyarki zaton tana cikin rahamar ubanginta domin macece mai yawan ibada dan Allah kuzama mai koyi da mahaifiyarki muddun kikai hakan to zaki rabauta Allah yaimaki albarka ya albarkaci rayuwar aurenku yakauda fitina a cikinta yahada kanku yadai daita tsakaninku, maza tashi kije kikwanta dare yayi.
Jiki a sanyaye tamike tana tafiya kamar kazarda kwai yafashema aciki binta yayi da kallo cikin tausayi da alhini hartakai bakin kofa ta juyo ganin yanayinshi yakara sanyaya mata jiki murmushin karfin hali taimashi tare da dagamai hannu alamar saida safe shima haka take a wurinshi.
Kwance take amma Sam barci ya kauracema idanunta sai faman juye juye take tunaninta daya yadda zata iya rayuwa da ya Abdallah Wanda duniya ba abunda ya tsana irinta bazata taba mance zuwanshi nakarshe ba irin wulakancin daya yimata.
Tafe suke itada kawarta jimmalo sanye suke cikin dagayen hijabbai milk in colour suna rataye da bag da alama daga makarantar islamiya suka dawo sai hirarsu suke cikin natsuwa subhanallahi shine abunda ta furta sakamakon jin saukar ruwan dake kwance gefen hanyar ajikinta, a hankali take bin jikinta da kallo ganin yadda gaba daya hijab din jikinta yakoma ja sannu a hankali motar tafara dawowa baya har ta iso inda suke tsaye budewa yayi yafito daniyar basu hakuri amma mi ganin kowa cece yasa yafara banbamin masifa inba dabbanciba taya zakuzo kutare ma mutane hanya sai kace kukadai akaima hanyar wlh kinyi Sa'a da banbi ta kankiba.
😧 baki kawai tasaki tana kallonshi batare datace kalaba jummalo ce tafaramai ruwan bala'i kasancewar ita ba kanwar lasa bace kuma bata barin kota kwana hannu tasa tarufe mata baki kada kema kizama jahila mana wadda batasan darajar Dan adam ba bakisan inkare na haushi ba a biyemashiba bashi ai gaba dayawa dagowa tayi taimai wani kallo andaiyi girman kwabo daga haka taja hannun jummalo sukai gaba,
In ranshi yayi dubu to yabace yanzu shi wannan yarinyar zata kalla tacema jahili, kare lallai wuyanta yayi kwari amma zaiyi maganinta cikin matsananci fushi yashiga mota tare da fizgarta kamar zaitashi sama,
Da mamaki jummalo tajuyo tana kallon Ariana ganin motar mutuminda yayi masu wulakanci ajiye a bakin gidansu dama kinsanshi kai kawai ta gyada mata alamar eh to amma ✋🏼 pls kada kice komi bayanda ta iya haka tai shiru Dan tasan halin kawartata saima yanzu fuskar guy din tadawo mata tabbas kobata tambayaba tasan dan uwantane ganin yadda suke matukar kama.
Da sallama tashiga cikin gidan Kai tsaye wurin G P dinda ke tsakar gidan ta nufa Bag dinta ta ajiye gefe sannan tacire hijab din jikinta ta wanke sannan tadauki bag dinta tanufi parlon ciki ciki tai sallama batare data kalli mutanen dake parlon ba hartakai bakin dakinta Umma tace wai Ariana miyasa kullun ina nuna maki amma baki fahimta kina kallon yayanki amma ko gaisuwa baki iyaba baki ta turo to Umma bakiganin yadda na dawo sai a lkcn ta lura dayanda duk jikinta yake jike da ruwa.
Cikin muryar damuwa tace yarinya kasancewar bata kiran sunanta miyasameki saida ta juyo ta harareshi kana tace wanine wanda baisan darajar dan adam ba,
A hartsuge yataso nikikecema bansan darajar dan adam ba saboda kin rainani ganin da gaske kanta yayo yasa ta kwada ihu tayi bayan ummanta tan gunguni cikin bacin rai umma ta zagayo da ita fada sosai tai mata kan rashin kunyar da taimashi cikin sanyin jiki tabar parlon tarasa miyasa Umma bata ganin laifinshi yanzu duk irin abunda yaimata amma Umma bataganiba batasan wace irin soyayyace tsakanin suba.
Haka takarace tunaninta tai bacci tana mai mikama Allah lamurranta dan tasan shikadai zai iya mata maganin damuwarta.

WELCOME TO SUNNAH BLOG

ANYTHING YOU ARE LOOKING FOR THIS IS HIS HOME *Hausa NOVELS of ANY kind *CIVIL ENGINEERING books *QUESTIONS on GLORIOUS QUR'AN AND MANY MORE
DON'T 4GET TO LIKE AND SHARE

Wednesday, 2 November 2016

SO ALJANNAR DUNIYA

SO ALJANNAR DUNIYA
NA HAFSATU M.A ABDULWAHEED

Written by Idress Adam Idress {SUNNAH}

Chapter 1

Page 1-5

Aure! Inna ni fa na gaya muku bazan auri kowa ba sai wanda nake so. Kuma yanzu ban ga abin da zai hana ku ba ni shi ba. Yana da mutunci da nutsuwa. Ba abin da zamu nuna musu. Kuma daidai muke tun da yana da asali, ba za ku yarda in zabi na kasa da ni ba? “Bodado mu ba mu hana ki zaben ki ba. Ba mu kuma ce ba shi da duk abin da kika ce yana da shi ba. Mu dai ba irinmu ba ne. Hanyoyinsu da dabi’o’insu da al’adunsu sun bambanta da namu.Yaya za a yi mu ba shi diyarmu? Ba ma haka ba, idan wata rana yace zashi garinsu yaya zamu hana shi tafiya da matarsa?” “Inna shi yariga ya san hanyoyinmu da al’adunmu da dabi’o’inmu. Nan aka haife shi, nan ya girma, ba abin da bai sani namu ba. In kuma har ya ce zai tafi da ni, to ni ba zan ki ba, domin ya nuna yana kauna ta kenan. Baya kuma kunyar shiga da ni ko’ina. Hasali ma, shi kansa bai taba zuwa ba?” Masu maganar suna hira a cikin dakin jinka ne, sai dai ya fi ywancin dakunan da ke gurin girma, kuma yana da kayan alatu irin na zamani kamar su gado, radiyo, leda da dai sauran ababen kawa. “Bodado kin dai nace akan Yasir. Zan je in gaya wa iyayenki. Shi babanki ba ruwansa tun da shi ardo (hakimi ko shugaba) ne, sai abin da dattijan gari suka ce. In da uwarki tana da rai, itace mai cewa komai. Allah ya jikan ta. Amin.” “Inna, ni da ma a ce ba komai muke ba, da sai kawai a daura mana aure; saura da me, ki lallashe shi. Zan je wajen fada wuro (uwar gida) ta sa mana baki. Kin kuma ce tace, in ya ga daidai ne, karba mata yake yi.” “Mhm ! wannan zamani, Allah ya sauwaka. Yarinya ki zauna kina zancen auranki, sai kace hirar nono da mai. Don haka fa ba ma son sa diyarmu makarantar boko. In kunyi karatu sai ku ce kunfi kowa. Me kuka dauke mu ne?” “Haba Inna ! In ba mu dauke komai ba, to wa za mu dauka komai? Inna in ba don karatu ba da yanzu ina sayar da nono. In yini ina yawo ga yunwa ga wahala, ga rashin sutura, da dan zane fingil. Yanzu fa dubi gidan nan. Da ni da gide da bamuyi karatu ba, ma gyara gidan nan? Ma kai Baba da goggo da Babba Makka. Badi kuma da ked a goggo karama. Inna ko kin san kudin da nake dauka a wata daya shi ne kudin da kike samu a shekara?” “Shekara Bodado ! Haba, wasa kike yi. Ni na san dai aikin da kike yi, na san kina samun kudi. Kun gama ginin dakunan da kuke yi? Mu ba mu san ko me za ku yi da su ba har yanzu.”
 “Gini da kuke gani wajen shan magani ne. Inna ni kam zan tafi yanzu; amma nayi miki alkawari zan zo har gida in gaya miki abin da muke nufi da shan magani.” Bodado ta fito tana tafe tana tunani tana sanye da zanen Fulani, amma har kasa rigar Fulani, rigar ta kame mata hakarkari. Bodado doguwa ce siririya. Tanada fuska mai kyawun gaske. gashinta dogone, bakikirin. Anyi masa ado da karafa irin na Fulani. Hannayanta da warawarai irin na azirfa. Tana da kyan fuska sai kace balarabiya. Duk wanda yahadu da ita sai yatsaya yana kallonta harsai ta bace. Gidan da ta shiga da darni ne, tai sallama ta shiga. “Goggo na gaya miki yawan aiki ba hutu yakansa tsufa da wuri.“ “Bodado, kincika surutu cha, cha, sai kace kwado. To, in ban yi aiki ba in yi me? Ina masu gida? Ina fata suna lafiya.” “goggo suna lafiya, ko kinyi kunun burdam.” (burdam wani irin kunu ne na madara). “Na ko yi da zan bayar a kowo miki. Amma gashi can cikin koko.” Bodado taje ta dauko ta zauna. 
“Dama ina nemanki, kinsan wai zamani ya sake sai an tambayeku ra,ayinku. Maigida yayi mana Magana, na kuma tura inna wajanki jiya ta kuma gaya mini yadda kukayi.” “Goggo kinsan duk abin da kika gaya wa baba yana ji. Ina so ki sa mani baki.” In yi me? Sa baki, raba ni da wuya. In ce masa kar ya aurad da ke, ni na Haifa masa ke? Haba Bodado har yanzu ba ki da wayo. In babanki ya ce zai yi abu ba abin da zai hana shi yi.” “Ni fa na gaya muku Goggo, Yasir nake so.” “Allah mai girma, har ya kawo mu zamani da yarinya za tace ga wanda takeso. To, naji na yarda, amma zai yarda, da al,ummu? Kuma me zamu cewa iyayen gidado? Tin kina yarinya suka kama wadansu. Indason ransu ne yanzu da sungoya jikoki.” “Goggo ho, su kama wadansu ni tunkiya ce ko akuya? In Allah bai bada haihuwar bafa? Gidado abokin yasir ne, muna son juna don haka bazai shiga btsakaninmu ba.” “bodado naji zanyi iy iyakar kokarina, amma ba dominki kadaiba na garko,dan uwarsa nasonki kwarai. Kullum muka hadu adduarta allah yasa ki auri danta. Na biyu, danta mai hankali ne da biyyaya, gashi kuma…….. bata gama Magana bodado ta rungumeta. “karki kada ni mana, ace ya takada babarta, nasan dma kinzo ne dan ki lallatsani, tashi ki tafi.” Ta fito daga gidan lokacin kuwa la’asar ta kusa sai ta haye reshe daya ta zauna, sai ga wani saurayi dogo fari ya zo ya tsaya a gindin itaciyar. Ta yi tsit ba ta motsa ba, tana kallon sa. Yana da doguwar fuska, idanunsa manya ne masu haske. Kuma kwayar rowan idon sa kasa-kasa ne. Yana da fuska mai kwarjini. Tana nan zaune ta kura masa ido har dai jikin sa ya bashi cewa akwai mai kallon sa. Ya daga ido sama ya ganta yayi murmushi. Ta diro suka zauna kan kututturen itace, tace, “Na yi zaton ko ba za ka zo ba.” “Haba na makara ne dan mun hadu da wasu abokaina shi ya sa. Ba kiyi hushi ba ko? Bodado yaya zancen aikin ku ne? Yaushe zaku ci gaba da aiki?” “Karshen watan nan ne, ai abokan aikin ma gobe wasu za su zo saboda kamala sauran shirye shiryen da dai sauran su.” “Madalla, wallahi kinyi kokari, mun kusa samun dakin shan magani. Ina taya ki murna.” “Na gode, ina fatan za ka zo in mun hada komai dad a komai ka ga kayan aikin da muke dashi.” “Zan zo in Allah ya so. Yaya maganar mu ne? Ina ma ace ke matata ce. In kin yarda zanje in ga baba gobe in kuma gaya wa Ummi ta je.” (Ummi uwa kenan da larabci) yana Magana yana wasa da kitson ta da karafan da ke kanta. “Na fi so ma kaje watakila baba yafi jin maganar mu in ya ganka amma wallahi ina jin tsoro ba dan na makara ba da naje makka na yi mana roko.” “Haba yanzu naji Magana ko anan ma Allah zai karbi rokon mu, da yardar Allah za mu samu nasara.” “Yas, (Abinda take kiran sa kenan) in ance sai ka shiga sharo fa?” “Shiga kai, me zai hana, ai ni nafi so ace in shiga din domin in tabbatar miki da soyayyata. Bodado, yanzu har kina shakkar son da nake yi miki. Wallahi, ko gaba daya cikin gabobin jikina aka ce in yanke ina yankewa.” “Ba haka bane ina jan kafarka ne. Irin so namu ba sai mun yi Magana ba. Tunda na tashi muke tare, amma banyi tunani zamu so juna ba said a na shiga sakandare aji daya. Ka tuna mun hadu wajen bikin sallah karama tun ran nan nake kaunar ka. Mutuwa kadai zata raba mu. Allah dai ya bamu so da sa’a. Amin.”