Ko kaifa banason kana cewa haka, idan kau har hakane to ta tabbata bamu muka haifesa bakenan ai yazamar masa dole yaso abunda mukeso yakuma bi umur ninmu matukar yanason gamawa da duniya lfy. Hakane yaya todan haka addu'ar ka kawai muke nema tare da fatan alheri,
Allah yasanya alkeri ya hada kansu yasa muce kara da akayi, Allah kuma yabar zumunci ameen ameen kanina,
To inaga tunda gobene za ai addu'ar bakwai sai ahada da daurin auren baki daya tunda ba abunda zamu tsaya jira Hakane Allah yakaimana rai goben, ameen.
Masha Allahu amma gaskiya alhj kayi tunani mai kyau kuma hakan shine daidai, dama tunanina gobe idan zamu wuce to bazan bartaba dole muwuce tare da ita to ashema tare da sarakuwata zanwuce gaskiya nayi matukar farin ciki dasa mun sarakuwa irin ariana kuma bakaramin dacen mata yaronnan yayiba , yarinya mai hankali da natsuwa bazaka taba cewa tashin kauye bace sosai mahaifiyarta tayi kokarin bata tarbiya maikyau, Allah sarki karima ashe bazakiyi tsawon raiba Allah ya gafarta maki yayi maki rahama yakuma kyautata makwancinki yasa halinki yabiki ameen.
Ariana zaune gaban abbanta kanta a kasa tana kokarin maida hawayenta, hannu yasa yadago kanta ariana kuka kike?
Kai ta girgiza alamar a'a auren ne bakiso? nanma kai ta girgiza to gayaman miyasa kike kuka shiru tayi batare da tace komiba yadade yana nazarinta kan yace ko yayan nakine baki so?
Da sauri tadaga mai kai alamar eh shiru yayi nadan wani lkc tabbas yasan ita da Abdallah basa shiri ko kadan hasalima basa shan inuwa daya kasan cewarshi mai tsananin son girma bazaka taba ganin dariyarshi ba muddun kannanshi nawurin amma bayan haka baisanshi da wani hali marar kyauba kuma da ace mahaifiyarta naraye ne datafi kowa farin ciki saboda akwai tsananin shakuwa da fahimtar juna tsakanibta da shi.
Baisan yadda zai karbi zancenba
Saidai fatanshi Allah ya daidaita tsakaninsu yasanya masu kaunar junansu.
To yishiru share hawayenki da sauri tasa hannunta tashiga share fuskarta, kinajina ko kai tadaga mashi
Banason kina cewa bakya son dan uwanki domin shi jininkine kuma garkuwa agareki sannan abun alfaharinki banason kina tada hankalinki akan abunda baikai yakawo ba insha Allahu bazaki taba dana saniba nasan dan uwanki bazai taba cutadda keba nasani zairikeki da amana bazai taba barin wani abu yasamekiba..
Amma abba aibaya sona hasalima ya tsaneni da bakinshifa yataba fadaman hakan to abba taya kake tunanin zai soni kuma har yayi zaman aure dani?
Abba dan Allah kada kabari a hadani dashi wlh mugune bayada tausayi baikamaci zama abokin rayuwataba abba dan Allah ka tausayaman,
Hannuwanta yakamo dake rike da kafafunshi ba abunda zanyi da yawuce inbaki hakuri inkuma yimaki addu'ar fatan alheri a duk inda kika kasance, kinfi kowa sanin banida kowa a duniyar nan da yawuce yaya shikadai yarageman dan haka dole in mashi biyayya inada tabbas din yaya bazai taba zama maki abunda zai cutar dake ba dan haka nike umurtarki dakizama mai biyayya, kizama mace tagari a cikin dakin aurenki mai hakuri gaduk wani abu da zaki gani matukar kikai hakuri to zaki cimma iyakar koma minene abu nagaba danike horonki dashi kizama mai rike sirrinki dana mijinki banason kizama cikin shasha shan matan dake fallasa sirrin gidan mazajensu duk runtsi kiyi kokarin rike sirrinki,
Maganar zaman takewa kuma basai nace maki komiba nasa mahaifiyarki tana koya maki wani abun kuma kema kina ganin yadda take tafiyar da rayuwar aurenta to inason kiyi koyi da ita dan ita macece tagari wadda kowane namiji zaiyi alfahari da samunta,
Cikin kankanin lkc yanayinsa ya chanja kwalla tacikamai ido cikin dubara ya gogeta batare daya bari yar tashi ta fahimci hakanba, tabbas ina kyautatama mahaifiyarki zaton tana cikin rahamar ubanginta domin macece mai yawan ibada dan Allah kuzama mai koyi da mahaifiyarki muddun kikai hakan to zaki rabauta Allah yaimaki albarka ya albarkaci rayuwar aurenku yakauda fitina a cikinta yahada kanku yadai daita tsakaninku, maza tashi kije kikwanta dare yayi.
Jiki a sanyaye tamike tana tafiya kamar kazarda kwai yafashema aciki binta yayi da kallo cikin tausayi da alhini hartakai bakin kofa ta juyo ganin yanayinshi yakara sanyaya mata jiki murmushin karfin hali taimashi tare da dagamai hannu alamar saida safe shima haka take a wurinshi.
Kwance take amma Sam barci ya kauracema idanunta sai faman juye juye take tunaninta daya yadda zata iya rayuwa da ya Abdallah Wanda duniya ba abunda ya tsana irinta bazata taba mance zuwanshi nakarshe ba irin wulakancin daya yimata.
Tafe suke itada kawarta jimmalo sanye suke cikin dagayen hijabbai milk in colour suna rataye da bag da alama daga makarantar islamiya suka dawo sai hirarsu suke cikin natsuwa subhanallahi shine abunda ta furta sakamakon jin saukar ruwan dake kwance gefen hanyar ajikinta, a hankali take bin jikinta da kallo ganin yadda gaba daya hijab din jikinta yakoma ja sannu a hankali motar tafara dawowa baya har ta iso inda suke tsaye budewa yayi yafito daniyar basu hakuri amma mi ganin kowa cece yasa yafara banbamin masifa inba dabbanciba taya zakuzo kutare ma mutane hanya sai kace kukadai akaima hanyar wlh kinyi Sa'a da banbi ta kankiba.
😧 baki kawai tasaki tana kallonshi batare datace kalaba jummalo ce tafaramai ruwan bala'i kasancewar ita ba kanwar lasa bace kuma bata barin kota kwana hannu tasa tarufe mata baki kada kema kizama jahila mana wadda batasan darajar Dan adam ba bakisan inkare na haushi ba a biyemashiba bashi ai gaba dayawa dagowa tayi taimai wani kallo andaiyi girman kwabo daga haka taja hannun jummalo sukai gaba,
In ranshi yayi dubu to yabace yanzu shi wannan yarinyar zata kalla tacema jahili, kare lallai wuyanta yayi kwari amma zaiyi maganinta cikin matsananci fushi yashiga mota tare da fizgarta kamar zaitashi sama,
Da mamaki jummalo tajuyo tana kallon Ariana ganin motar mutuminda yayi masu wulakanci ajiye a bakin gidansu dama kinsanshi kai kawai ta gyada mata alamar eh to amma ✋🏼 pls kada kice komi bayanda ta iya haka tai shiru Dan tasan halin kawartata saima yanzu fuskar guy din tadawo mata tabbas kobata tambayaba tasan dan uwantane ganin yadda suke matukar kama.
Da sallama tashiga cikin gidan Kai tsaye wurin G P dinda ke tsakar gidan ta nufa Bag dinta ta ajiye gefe sannan tacire hijab din jikinta ta wanke sannan tadauki bag dinta tanufi parlon ciki ciki tai sallama batare data kalli mutanen dake parlon ba hartakai bakin dakinta Umma tace wai Ariana miyasa kullun ina nuna maki amma baki fahimta kina kallon yayanki amma ko gaisuwa baki iyaba baki ta turo to Umma bakiganin yadda na dawo sai a lkcn ta lura dayanda duk jikinta yake jike da ruwa.
Cikin muryar damuwa tace yarinya kasancewar bata kiran sunanta miyasameki saida ta juyo ta harareshi kana tace wanine wanda baisan darajar dan adam ba,
A hartsuge yataso nikikecema bansan darajar dan adam ba saboda kin rainani ganin da gaske kanta yayo yasa ta kwada ihu tayi bayan ummanta tan gunguni cikin bacin rai umma ta zagayo da ita fada sosai tai mata kan rashin kunyar da taimashi cikin sanyin jiki tabar parlon tarasa miyasa Umma bata ganin laifinshi yanzu duk irin abunda yaimata amma Umma bataganiba batasan wace irin soyayyace tsakanin suba.
Haka takarace tunaninta tai bacci tana mai mikama Allah lamurranta dan tasan shikadai zai iya mata maganin damuwarta.
No comments:
Post a Comment