NA HAFSATU M.A ABDULWAHEED
Written by Idress Adam Idress {SUNNAH}
Page 1-5
Aure! Inna ni fa na gaya muku bazan auri kowa ba sai wanda nake so. Kuma yanzu ban ga abin da zai hana ku ba ni shi ba. Yana da mutunci da nutsuwa. Ba abin da zamu nuna musu. Kuma daidai muke tun da yana da asali, ba za ku yarda in zabi na kasa da ni ba? “Bodado mu ba mu hana ki zaben ki ba. Ba mu kuma ce ba shi da duk abin da kika ce yana da shi ba. Mu dai ba irinmu ba ne. Hanyoyinsu da dabi’o’insu da al’adunsu sun bambanta da namu.Yaya za a yi mu ba shi diyarmu? Ba ma haka ba, idan wata rana yace zashi garinsu yaya zamu hana shi tafiya da matarsa?” “Inna shi yariga ya san hanyoyinmu da al’adunmu da dabi’o’inmu. Nan aka haife shi, nan ya girma, ba abin da bai sani namu ba. In kuma har ya ce zai tafi da ni, to ni ba zan ki ba, domin ya nuna yana kauna ta kenan. Baya kuma kunyar shiga da ni ko’ina. Hasali ma, shi kansa bai taba zuwa ba?” Masu maganar suna hira a cikin dakin jinka ne, sai dai ya fi ywancin dakunan da ke gurin girma, kuma yana da kayan alatu irin na zamani kamar su gado, radiyo, leda da dai sauran ababen kawa. “Bodado kin dai nace akan Yasir. Zan je in gaya wa iyayenki. Shi babanki ba ruwansa tun da shi ardo (hakimi ko shugaba) ne, sai abin da dattijan gari suka ce. In da uwarki tana da rai, itace mai cewa komai. Allah ya jikan ta. Amin.” “Inna, ni da ma a ce ba komai muke ba, da sai kawai a daura mana aure; saura da me, ki lallashe shi. Zan je wajen fada wuro (uwar gida) ta sa mana baki. Kin kuma ce tace, in ya ga daidai ne, karba mata yake yi.” “Mhm ! wannan zamani, Allah ya sauwaka. Yarinya ki zauna kina zancen auranki, sai kace hirar nono da mai. Don haka fa ba ma son sa diyarmu makarantar boko. In kunyi karatu sai ku ce kunfi kowa. Me kuka dauke mu ne?” “Haba Inna ! In ba mu dauke komai ba, to wa za mu dauka komai? Inna in ba don karatu ba da yanzu ina sayar da nono. In yini ina yawo ga yunwa ga wahala, ga rashin sutura, da dan zane fingil. Yanzu fa dubi gidan nan. Da ni da gide da bamuyi karatu ba, ma gyara gidan nan? Ma kai Baba da goggo da Babba Makka. Badi kuma da ked a goggo karama. Inna ko kin san kudin da nake dauka a wata daya shi ne kudin da kike samu a shekara?” “Shekara Bodado ! Haba, wasa kike yi. Ni na san dai aikin da kike yi, na san kina samun kudi. Kun gama ginin dakunan da kuke yi? Mu ba mu san ko me za ku yi da su ba har yanzu.”
“Gini da kuke gani wajen shan magani ne. Inna ni kam zan tafi yanzu; amma nayi miki alkawari zan zo har gida in gaya miki abin da muke nufi da shan magani.” Bodado ta fito tana tafe tana tunani tana sanye da zanen Fulani, amma har kasa rigar Fulani, rigar ta kame mata hakarkari. Bodado doguwa ce siririya. Tanada fuska mai kyawun gaske. gashinta dogone, bakikirin. Anyi masa ado da karafa irin na Fulani. Hannayanta da warawarai irin na azirfa. Tana da kyan fuska sai kace balarabiya. Duk wanda yahadu da ita sai yatsaya yana kallonta harsai ta bace. Gidan da ta shiga da darni ne, tai sallama ta shiga. “Goggo na gaya miki yawan aiki ba hutu yakansa tsufa da wuri.“ “Bodado, kincika surutu cha, cha, sai kace kwado. To, in ban yi aiki ba in yi me? Ina masu gida? Ina fata suna lafiya.” “goggo suna lafiya, ko kinyi kunun burdam.” (burdam wani irin kunu ne na madara). “Na ko yi da zan bayar a kowo miki. Amma gashi can cikin koko.” Bodado taje ta dauko ta zauna.
“Dama ina nemanki, kinsan wai zamani ya sake sai an tambayeku ra,ayinku. Maigida yayi mana Magana, na kuma tura inna wajanki jiya ta kuma gaya mini yadda kukayi.” “Goggo kinsan duk abin da kika gaya wa baba yana ji. Ina so ki sa mani baki.” In yi me? Sa baki, raba ni da wuya. In ce masa kar ya aurad da ke, ni na Haifa masa ke? Haba Bodado har yanzu ba ki da wayo. In babanki ya ce zai yi abu ba abin da zai hana shi yi.” “Ni fa na gaya muku Goggo, Yasir nake so.” “Allah mai girma, har ya kawo mu zamani da yarinya za tace ga wanda takeso. To, naji na yarda, amma zai yarda, da al,ummu? Kuma me zamu cewa iyayen gidado? Tin kina yarinya suka kama wadansu. Indason ransu ne yanzu da sungoya jikoki.” “Goggo ho, su kama wadansu ni tunkiya ce ko akuya? In Allah bai bada haihuwar bafa? Gidado abokin yasir ne, muna son juna don haka bazai shiga btsakaninmu ba.” “bodado naji zanyi iy iyakar kokarina, amma ba dominki kadaiba na garko,dan uwarsa nasonki kwarai. Kullum muka hadu adduarta allah yasa ki auri danta. Na biyu, danta mai hankali ne da biyyaya, gashi kuma…….. bata gama Magana bodado ta rungumeta. “karki kada ni mana, ace ya takada babarta, nasan dma kinzo ne dan ki lallatsani, tashi ki tafi.” Ta fito daga gidan lokacin kuwa la’asar ta kusa sai ta haye reshe daya ta zauna, sai ga wani saurayi dogo fari ya zo ya tsaya a gindin itaciyar. Ta yi tsit ba ta motsa ba, tana kallon sa. Yana da doguwar fuska, idanunsa manya ne masu haske. Kuma kwayar rowan idon sa kasa-kasa ne. Yana da fuska mai kwarjini. Tana nan zaune ta kura masa ido har dai jikin sa ya bashi cewa akwai mai kallon sa. Ya daga ido sama ya ganta yayi murmushi. Ta diro suka zauna kan kututturen itace, tace, “Na yi zaton ko ba za ka zo ba.” “Haba na makara ne dan mun hadu da wasu abokaina shi ya sa. Ba kiyi hushi ba ko? Bodado yaya zancen aikin ku ne? Yaushe zaku ci gaba da aiki?” “Karshen watan nan ne, ai abokan aikin ma gobe wasu za su zo saboda kamala sauran shirye shiryen da dai sauran su.” “Madalla, wallahi kinyi kokari, mun kusa samun dakin shan magani. Ina taya ki murna.” “Na gode, ina fatan za ka zo in mun hada komai dad a komai ka ga kayan aikin da muke dashi.” “Zan zo in Allah ya so. Yaya maganar mu ne? Ina ma ace ke matata ce. In kin yarda zanje in ga baba gobe in kuma gaya wa Ummi ta je.” (Ummi uwa kenan da larabci) yana Magana yana wasa da kitson ta da karafan da ke kanta. “Na fi so ma kaje watakila baba yafi jin maganar mu in ya ganka amma wallahi ina jin tsoro ba dan na makara ba da naje makka na yi mana roko.” “Haba yanzu naji Magana ko anan ma Allah zai karbi rokon mu, da yardar Allah za mu samu nasara.” “Yas, (Abinda take kiran sa kenan) in ance sai ka shiga sharo fa?” “Shiga kai, me zai hana, ai ni nafi so ace in shiga din domin in tabbatar miki da soyayyata. Bodado, yanzu har kina shakkar son da nake yi miki. Wallahi, ko gaba daya cikin gabobin jikina aka ce in yanke ina yankewa.” “Ba haka bane ina jan kafarka ne. Irin so namu ba sai mun yi Magana ba. Tunda na tashi muke tare, amma banyi tunani zamu so juna ba said a na shiga sakandare aji daya. Ka tuna mun hadu wajen bikin sallah karama tun ran nan nake kaunar ka. Mutuwa kadai zata raba mu. Allah dai ya bamu so da sa’a. Amin.”
No comments:
Post a Comment