Na Abdul-Aziz Sani M/GINI
Written by
2 EFFECT
SUNNAH
&
TEEMERH NEW
1⋐⋑5
A wani zamani can baya mai tsawo da ya shuɗe, anyi wani shahararren sarkin Musulunci wanda ya shekara ɗari da sittin akan karagar mulki, ana kiransa da suna Uwaisul Karni. Har tsufa ya riski Sarki Uwaisul karni matan sa biyu kacal, kuma 'ya'yansa biyu dukkan su maza sa'annin juna. Ana kiran waɗannan 'ya'ya nasa da UKASHAT da UZAIFAT .
Mahaifiyar Ukashat ita ce Uwar gida. Ukashat da Uzaifat sun taso da tarin ilimi, hankali da sanin ya kamata, sannan kuma kowannensu ya kasance Sadauki kuma barde dodon maza a filin yaki, wanda har ta kai an kasa banbancewa wanda ya fi wani karfi da jarumtaka a tsakanin su.
Yayin da tsufa ya riski sarki Uwaisul Karni sai matansa Shulaifa da Muzaira suka fara kishi akan kowacce ta fi so ɗanta ya gaji Sarki. A dalilin haka ne suka dukufa wajen Ziyartar Malamai domin bukatarsu ta biya.
🔯🔯🔯
A can nesa da birnin DARUL HUSUF, wato birnin Sarki Uwaisul Karni, akwai wata babbar kasa ta kafirai wacce ta gagari Sarki Uwaisul Karni, domin sau tara yana yaki da su amma sai dai ayi KARE JINI, BIRI JINI. Sunan kasar SHUMBUL, kuma sunan sarkin su Sharan Ibini Nukaib.
Lokacin da sarki Uwaisul karni ya fahimci cewa Ukashat da Uzaifat sun tada hankalinsu akan su gaje shi saboda kowanne ya ɗauki zugar mahaifiyarsa sai ya kira su ya ce da su:
"Ya ku 'ya'yana kuyi sani cewa bani da wani buri a duniya wanda yafi naga na ci birnin shumbul da yaki kafin cikar ajalina, bisa wannan dalili ne na umarceku da kuje kowannen ku ya shirya DAKARUN MUSULUNCI nasa mataimakansa waɗanda basa yin aikin Alfasha, basa shan giya, basa yin zina, waɗanda basu taɓa saɓon Ubangijin Musulunci ba, kowannenku ya taro nasa mataimakan duk wanda ya sami nasarar yaki akan kasar shumbul daga cikin ku shine zai gaje ni".
Koda jin wannan batu sai Uzaifaf da Ukashat suka yi murna, suka yi farin ciki da jin wannan batu. Domin lokaci yayi da zasu nunawa duniya cewa Musulunci ba kanwar lasa ba ne. Anan suka yi alkawarin lalle sai sun cikawa mahaifinsu burinsa. Nan take kowannensu ya fara shirye-shirye, suna masu shirya dakarun yaki kuma DAKARUN MUSULUNCI.
Dama sarki Uwaisul Karni ya basu izinin kowannensu ys tara dakaru dubu ɗari uku kaɗai.
Ukashat ne ya fara haɗa tasa rundunar inda yai sauri ya ɗebe dukkanin manyan Dakarun kasar waɗanda ake takama dasu a fagen fama, wato waɗanda suka fi jarumtaka, juriya da jajircewa. Lokacin da Ukshat ke zaɓo waɗannan zaratan Dakaru baiyi la'akari da bayanin mahaifinsu ba na cewa lalle su zaɓo daga masu kwatanta gaskiya da tsoron Allah. In dai ya fahimci cewa mutum barde ne kawai sai ya zaɓe shi.
A lokacin da Uzaifat yazo zai zaɓi nasa dakarun sai yaga ashe Ukashat yai masa shigar sauri, ya kwashe manyan baraden kasar waɗanda sune dirkar birnin masu ciyo yaki. Hatta sarkin yakin Kasar kuwa Salahuddeen Ayubi. Al'amarin da ya dugunzuma hankalinsa kenan, har ya ji gwiwarsa tayi sanyi, amma duk da haka bai fasa zaɓo nasa dakarun ba waɗanda basu kasance zakwakurai ba, amma kuma suna da karfin imani gami da tsoron Allah. Ya fitar da shugaba a cikinsu wanda babu kamar sa a jarumta, ana kiran sa da suna Abul Shaja'a.
Bayan Uzaifat ya gama haɗa wannan runduna wadda Abul Shaja'a ke jagoranta sai suka fara fita bayan gari kullum suna bawa kansu horon yaki domin su tabbatar da cewa anyi kyakkyawan shiri kafin zuwa ranar da zasu fara fita su tari abokan gaba. A can ɓangaren Dakarun Ukashat kuwa, ko sau ɗaya basu taɓa tunanin su fita yin horo ba saboda sun yarda da kansu, sun san cewa ko daga bacci suka tashi zasu iya tarar yaki.
A ranar da su Uzaifat suka cika kwana bakwai suna baiwa kansu horon yakin ne labari ya riski su Ukashat. Al'amarin da ya basu dariya kenan.
Ukashat ya dubi Sarkin yaki Salahuddeen ya ce "Ya kai dirkar Darul Hasuf kaji cewa su Uzaifat sun dukufa wajen baiwa kansu horon yaki har tsawon kwana bakwai kenan yau. An ya kuwa ba ma kai musu ziyarar ba zato ba, domin mu auna iyakar kokarinsu da namu. Ka san ance ɗan hakin da ka raina shi kan tsone maka ido. Kada fa muyi sakaki su bamu mamaki, wato su sami nasarar wannan yaki da za a yi da mutanen Shumbul".
Koda jin wannan batu sai Sarkin Yaki Salahuddeen Ayubi ya bushe da dariya ya ce, "Ranka ya daɗe in banda abinka yaya gara za tayi da zago? Shin ka manta da yawan mayakan birnin Shumbal ne da kuma yawan yawan zakwakuran dakarunsu ne, ai duk irin horon da su Abu Shaja'a zasu samu ba za su taɓa samun nasara ba a kansu. Mu ma kanmu nan sai munyi da gaske, mun yi tunanin sabbin dakarun da ya kamata muyi amfani dasu. Ka sani cewa a cikin mayakan birnin Shumbal akwai wani gawurtaccen barde da ya fara fitowa yaki a shekaru uku baya. Wannan barde shi nafi shakka fiye da kowa, kuma babu yadda za ayi mu sami nasara akan mutanen Shumbal face mun gama da barden."
Yayin da Ukashat yaji wannan batu sai ya jinjina kai ya ce, "Menene sunan barden, kuma ya za ayi na shaida shi idan muka fita yakin? Ima son ka barni da shi, ina tabbatar maka da cewa ni zan kashe shi komai karfin Jarumtakarsa."
Da jin wannan batu sai Salahuddeen Ayubi yai dariya ya ce "Ya kai yarima Ukashat ka sani cewa sau uku ina tarar wannan barde fa muna yin ragas, ban taɓa samun nasara akansa ba, shima haka. Ta ya ya kake tsammanin cewa kai zaka iya dashi?"
Ukashat yayi murmushi ya ce, "Ina da tabbacin zan iya samun nasara a kanka, ka ga kenan idan har zan samu a kanka lalle zan samu a kansa. Na fuskanci cewa saboda bamu taɓa fita yaki ba ni da Uzaifat shi ya sa ba a san iyakar jarumtakarmu ba, sai iya wadda aka ga mun nuna anan gida. Idan kana shakkar abinda na faɗa yanzu mu jarraba fidda raini yanzu ni da kai"
6 ♦10
Sa'adda Sarkin yaki Salahuddeen Ayubi yaji haka, sai ransa ya ɓaci, zuciyarsa ta kama tafarfasa ya ce a ransa _"Yanzu wannan karamin yaron Ukashat da ya girma a gaba na shine yake ganin cewa zai iya karo da ni? Lalle kuwa yau zan nuna masa cewa bakin rijiya ba wajen wasan yaro bane."_
Koda gama aiyana hakan a ransa sai ya zare takobinsa ya sauko daga kan dokinsa a fusace ya nufi Ukashat. Abinda ya ɗaurewa sauran Dakarun kai shine, Ukashat ba zare tasa takobin ba bare ma ya sauko daga kan nasa nasa dokin, kawai sai ya ci gaba da zamansa yana mai sauraron isowar Salahuddeen. Ai kuwa Salahuddeen na isowa sai ya kai masa wawan sara a wuya. Cikin matukar zafin nama Ukashat ya sunkuya takobin ya sari Iska.
Kafin Salahuddeen ya sake kai wani saran tuni Ukashat yai tsalle sama daga kan dokinsa tamkar an janyeshi da kugiya kawai sai ya jerawa Salahuddeen duka da Kafa a kirji sau uku yana a saman kamar tsuntsu. Duk da cewa Salahuddeen murjejen kari ne mai kirar sadaukantaka sai da yayi baya taga-taga zai faɗi, amma saboda taurin rai da zuciya sai ya dage ya tsaya cak a waje guda. A sannan ne fa gaba ɗayan dakarun suka kaure da kabbara bisa mamakin ganon jarumtakar da Ukashat yayi.
Shi kansa Salahuddeen yai mamaki, duk da cewa ya sha ganin yadda Ukashat da Uzaifat ke dakawa maza gumba a hannu a cikin gari, amma da yake suna shakkarsa sai yayi tsammanin cewa ba zaau iya karawa da shi ba. Abin da bai sani ba shine kawai suna girmamashi ne a matsayinsa na Sarkin Yaki kuma basa so su kunyatashi.
Ukashat ya diro kasa a bayan Salahuddeen ya zare tasa takobin suka fara zagaya juna suna kallon kallo tamkar Zaki da Zaki zasu kafsa. Kawai sai suka kacame da azababben yaki suna masu kaiwa juna *SARA DA SUKA* cikin zafin nama, juriya da bajinta tamkar masu jikin karfe saboda sauri. Nan fa dakaru suka zuba ido suna kallon ikon Allah suna al'ajabi, domin a tarihin sadaukantakar Salahuddeen ba a taɓa samun mutumin da ya fafata da shi ba tsawon dakika ɗari da tamanin ba tare da ya kaishi kasa ba, sai wannan bakon barde na birnin Shambul, amma yanzu gashi Ukashat na neɓan gagararsa.
Abu dai kamar wasa sai gashi an sake shafe rabin sa'a ana wannan fafatawa amma duk a tsawon lokacin ko sau ɗaya Salahuddeen bai sami damar yankar jikin Ukashat ba ko sukarsa. Al'amarin da ya kara fusatashi kenan ya kara kaimi. Yayin da Ukashat ya ga haka sai yayi wata irin alkafira da baya-baya ya nisanta da Salahuddeen ya tsaya daga nesa kaɗan fuskarsa cike da murmushi yace, "Ya kai Sarkin yaki kayi sani cewa na baka dama har tsawon sama da rabin sa'a ba ka iya cutar dani ba, to yanzu gani nan bisa kanka nima zanyi amfani da tawa damar."
Kafin Sarkin yaki Salahuddeen yayi wani yunkuri tuni Ukashat ya daka tsalle ya dira a gabansa kamar ɗaukoshi akayi aka ajiye. Nan fa ya shiga kaiwa Salahuddeen mummunan sara da suka. Tsanannin karfin harin yasa Salahuddeen kasa mai da martani, sai kawai ya ci gaba da kare kai. A duk sa'adda Ukashat ya sami damar cutar da Salahuddeen sai ya ki cutar dashi dan yayi dariya kawai. A haka suka ci gaba da artabu har Ukashat ya kaishi kas kuma ya buge takobinsa ta faɗi kas ya tsirashi da tasa. Kawai sai sauran Dakarun suka ruɗe da kabbara suna yiwa Ukashat jinjina cikin matukar al'ajabi.
Ukashat ya juyawa Salahuddeen baya ya tafi izuwa dokinsa ya kama ya hau, sannan ya juyo ya dubeshi ya ce, "ku biyoni a baya mu tafi izuwa bayan gari inda su Uzaifat ke baiwa kansu horo."
Gama faɗin haka ke da wuya sai Ukashat ya sakarwa dokinsa linzami ya sukwaneshi da gudu ya bar harabar gidan sarautar. Cikin alamun kunya da matukar takaici sarkin yaki Salahuddeen ya mike tsaye ya hau kan nasa dokin a lokacin da kwallar takaici ta cika idanunsa, amma kuma da ya ga sauran Dakarun sun tsaitsaya a bayansa sai da ya hau dokinsa yai gaba sannan suka take masa baya sai yaji daɗi a ransa, domin ya fahimci cewa har yanzu yana da sauran kima da martaba a idanunsu duk da cewa yarima Ukashat ya kaskantar da shi a gabansu
Sarkin yaki Salahuddeen da sauran Dakarun suka zaburi dawakansu a guje har suka cimma Ukashat, ya zamana cewa Ukashat da Salahuddeen sun kusan haɗa kafaɗa. A sannan ne Ukashat ya dubi Salahuddeen ya ce "Ka gafarceni ya dirkar Darul Husuf, kayi sani cewa bani da niyyar kaskantarka akan idon kowa."
Koda jin wannan batu sai Salahuddeen yaji zuciyarsa tayi sanyi ya maida masa martanin murmushi sannan yace, "Ya shugabana ai kome kayi mini ba zai taɓa zama laifi ba, domin kaine sarkin gobe. Fatana shine idan har bukata ta biya na zamo mukasanci a gareka."
Sa'adda Ukashat yaji haka sai ya bushe da dariya, daga can kuma sai ya haɗe fuska yace, "idan har ka taimaka mun wannan runduna tamu ta ci birnin shumbul da yaki nayi maka alkawari kaine zaka zama wazirina yayin da na zama Sarkin Darul Husuf."
Koda jin haka sai Salahuddeen ya cika da tsananib farin ciki, ya kara bakinsa daf dana yarima Ukashat yace, "Ai kuwa ko da zan kauce hanya sai na kauce muddin bukatarmu zata biya, saboda haka ka kwantar da hankalinka komai rintsi da tsanani kai ne zaka hau karagar Sarki, ba dai Uzaifat ba sai dai idan bana numfashi a doron kasa."Sarkin yaki Salahuddeen da sauran Dakarun suka zaburi dawakansu a guje har suka cimma Ukashat, ya zamana cewa Ukashat da Salahuddeen sun kusan haɗa kafaɗa. A sannan ne Ukashat ya dubi Salahuddeen ya ce "Ka gafarceni ya dirkar Darul Husuf, kayi sani cewa bani da niyyar kaskantarka akan idon kowa."
Koda jin wannan batu sai Salahuddeen yaji zuciyarsa tayi sanyi ya maida masa martanin murmushi sannan yace, "Ya shugabana ai kome kayi mini ba zai taɓa zama laifi ba, domin kaine sarkin gobe. Fatana shine idan har bukata ta biya na zamo mukasanci a gareka."
Sa'adda Ukashat yaji haka sai ya bushe da dariya, daga can kuma sai ya haɗe fuska yace, "idan har ka taimaka mun wannan runduna tamu ta ci birnin shumbul da yaki nayi maka alkawari kaine zaka zama wazirina yayin da na zama Sarkin Darul Husuf."
Koda jin haka sai Salahuddeen ya cika da tsananib farin ciki, ya kara bakinsa daf dana yarima Ukashat yace, "Ai kuwa ko da zan kauce hanya sai na kauce muddin bukatarmu zata biya, saboda haka ka kwantar da hankalinka komai rintsi da tsanani kai ne zaka hau karagar Sarki, ba dai Uzaifat ba sai dai idan bana numfashi a doron kasa."
'Yan uwan biyu na haduwa suka kaure da azababben artabu, ya zamana cewa suna kaiwa juna sara da suka cikin zafin nama, juriya da bajinta.
Wohoho! Idan sadaukantaka ta hadu da takwararta dole ne idanu su more kallo. Lokacin da wannan gumurzu ya dan yi nisa sai hankalin gaba daya Dakarun da ke wajen ya dugunzuma ainun, domin tsanani ya kai tsanani, ga dukkan alamu ba za a gama lafiya ba ba tare da an salwantar da rayuwar daya ba. Domin yadda suke kaiwa juna hari tamkar kafiri da musulmi sun hadu, kowannensu bil hakki yake fadan kuma a fusace suna kokarin ganin bayan juna.
Koda aka shafe rabin sa'a ana wannan fafatawa sai suka ja da baya a lokaci guda suka ba da tazarar taku biyar-biyar, sannan suka rugo ga juna cikin mugun nufi. Tun kafin su hadu hankalin kowa dake wajen ya kara dugunzuma, domin an san cewa in dai aka hadu karon ba zai yi kyau ba. Ko da ya rage saura taku daya su hadu sai suka daka tsallesuka yi sama a lokaci guda suka kaiwa juna sara da takobi. Kowa sai ya sami nasara suka yanki damatsan hannayensu, jikinsu ya dare jini ya zuba suka rikito kasa suna masu dafe raunukan.
11⋐⋑15
Da jin haka sai shima Ukashat ya cika da murna suka ci gaba
da hira cikin nishadi har suka iso bayan gari inda su Uzaifat suka yada
sanasani suka kafe tantuna. Da zuwa kuwa sai suka iske Uzaifat tare da
dakarunsa yana tsaye a tsakiyarsu sun yi masa da’ira yana koya musu yadda ake
sarrafa takobi a tsakiyar abokan gaba, harma yana umartar wasu daga cikinsu da
su afka masa. Da zarar sun afka masa sai su ga ya tarwatsasu nan da nan. Suna
cikin wannan hali ne kawai sai suka hango kurar dawakan su Ukashat daga nesa kadan
don haka sai suka tsaya suna jiran isowarsu don su ga ko su waye. In ba don ma
sun ga cewa daga cikin gari suka fito da sai suyi tsammanin ko abokan gaba ne
suka kawo farmakin sumame.
Lokacin da su Ukashat suka karaso aka ga juna sai mamaki ya
kama Uzaifat ya dubi Ukashat y ace, “Lale marhabun da dan Uwa rabin jiki. Shin
kun zo ne ku bamu gudunmawa bias kokarin da muke yi?”.
Ukashat ya kada kai alamar cewa ba wannan ce ta kawo su ba,
sannan yace, “Mun zo ne mu yi liken asirinku mu saci irin salon yakin da kuka
tanada”.
Ko da gama fadin haka sai mamaki ya kama Uzaifat da
jama’arsa, domin sun san cewa basu fi su Ukashat iya yaki ba, asali ma ko tafin
hannunsu ba su kai ba.
Ukashat da jama’arsa suka bushed a
dariya, al’amarin da ya sosa zuciyar Uzaifat kenan. Amma sai ya dubi Ukashat
yace, “Ya kai dan uwana ina son ku bar wajen nan kai da jama’arka ku kyalemu mu
yi abinda ke gabanmu mu da ku kowa tasa ta fishsheshi.”
Ukashat ya gyada kai yana mai yin
murmushin mugunta yace, “Ba zai yiwu ba muzo har nan kuma mu tafi a banza. Mun
zo ne domin jama’ata da taka su gwada ‘yar kasha domin a bambance tsakanin aya
da tsakuwa, asan wadanda ya kamata a tura yaki ba sai an tsaya bata lokaci ba”.
Cikin fushi Uzaifat ya dakawa
Ukashat tsawa yace, “Wannan ai zancen banza ka ke yi, domin kuwa bah aka
Abbanmu ya shirya ba. Cewa yayi ni da kai kowannenmu ya shirya dakarunsa dabam,
kuma dukkaninmu zamu je wannan yaki, bai zaba ba”.
Ukashat yai dariya sannan yace
“Wannan gaskiya ne, haka Abbanmu ya tsara amma kuma nima yanzu nazo da nawa
tsarin kuma dole haka za a yi”.
Koda gama fadin haka sai Ukashat ya
dubi su Sarkin yaki Salahuddeen yace “Ku afka musu ku maishe da su nakasassu
yadda ba za su iya fita yaki ba.”
Koda jin wannan Umarni sai su
Salahuddeen suka zare makamansu da nufin su afkawa su Uzaifat, amma sai Uzaifat
yayi wuf ya sha gabansu yace “Ku fara gamawa da ni kafin su”.
Da jin haka sai su Salahuddeen suka
dan ja baya domin sun san cewa abu ne mai hadarin gaske idan dayansu ya kuskura
ya taba lafiyar yarima Uzaifat.
Ukashat ya dakawa su Salahuddeen
tsawa yace, “Me kuke jira ne dashi? Ku afka masa kawai, umarnina ne ban a kowa
ba”. Cikin sanyin jiki da alamar karayar zuciya Sarkin yaki Salahuddeen ya dubi
Ukashat yace, “Ya shugabana kai ma ka san cewa duk wanda ya taba yarima daga
cikinmu zai fuskanci fushin sarki. Ina ganin cewa zai fi kyau mu hakura da
wannan shiri mu koma cikin gari”.
Koda jin wannan furuci sai Ukashat
ya fusata, ya zare takobinsa ya nufi Uzaifat gadan-gadan yana mai cewa, “Ni
bari na nuna muku misali ku ga zahiri, don ku san cewa baba wargi a cikin
lamarina”.
Lokacin da Uzaifat ya ga dan uwansa
Ukashat ya taho kansa rike da takobi tsirara cikin mugun nufi sai shima ya zare
tasa takobin ya tare shi a lokacin da gaba daya dakarun da ke wajen suka nutsu
suka tattara hankulansu kowa a kansu.
Amma saboda juriya da jarumtaka basu nuna wata gazawa ba, sai kawai suka sake yunkurawa suka ruga ga juna.
Cikin zafin nama Sarkin yaki Salahuddeen ya daka tsalle ya dira a tsakiyarsu, bai bari sun hadu ba. Cikin fushi Ukashat ya dakawa Salahuddeen tsawa yace, "Saboda me zaka katse mana wannan fada?".
Salahuddeen ya risina sannan yace, "Ka gafarceni ya shugabana, kayi sani cewa idan muka bari kuka lahanta junanku sosai fushin mahaifinku zai tabbata akanmu. Idan kaga mun barku kun ci gaba da wannan gasa sai dai idan bama numfashi a doron kasa."
Sa'adda Ukashat yaji wannan batu sai takaici ya kamashi ya rasa abinda ke masa dadi a duniya, kawai sai ya yi tsaki ya juya ya tafi ga dokinsa ya kamashi ya hau ya sukwaneshi a guje.